Рет қаралды 22,871
Shin mulkin soji zai iya share wa mutanen Jamhuriyar Nijar hawaye? Wadanne dalilai ne ya kamata ayi laakari da su domin guje wa salon mulkin sojoji ?
A cikin shirin Gaskiyar Magana na yau mun shirya gudanar da muhawara kan wannan maudu’i, inda muka gayyato muku Abdoulaziz M Taya , babban jami’in kuingiyar farar hula ta (MRSP) mai goyon bayan mulkin soji a Nijar da kuma Boubacar Dan Zourmani, dan siyasa da ke adawa da juyin mulki a wannan kasa da ke Afirka ta Yamma